Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

“Ƙauna Ba Ta Jin Daɗin Mugunta”

“Ƙauna Ba Ta Jin Daɗin Mugunta”

Kiristoci na gaske suna nuna ƙauna a dukan abubuwan da suke yi. “Ƙauna ba ta jin daɗin mugunta.” (1Ko 13:​4, 6) Saboda haka, muna guje wa nishaɗin da ake nuna lalata da mugunta. Ƙari ga haka, ba ma farin ciki sa’ad da mutane suka faɗa cikin matsala, ko da waɗanda suka yi mana laifi ne.​—K. Ma 17:5.

KU KALLI BIDIYON NAN KADA MU MANTA YADDA ƘAUNA TAKE​—BA TA JIN DAƊIN MUGUNTA, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Mene ne Dauda ya yi sa’ad da ya ji cewa Saul da Jonathan sun mutu?

  • Wace waƙa ce Dauda ya rera don Saul da Jonathan?

  • Me ya sa Dauda bai yi farin ciki ba sa’ad da ya ji cewa Saul ya mutu?