RAYUWAR KIRISTA
“Ƙauna Takan . . . Sa Zuciya Cikin Kowane Hali”
Ƙauna ce take sa mu sa rai cewa ’yan’uwanmu za su yanke shawarwari masu kyau. (1Ko 13:4, 7) Alal misali, idan wani ɗan’uwa ya yi zunubi kuma aka yi masa horo, muna fatan cewa zai amince da yadda ake ƙoƙari a taimaka masa. Muna haƙuri da waɗanda bangaskiyarsu ta yi sanyi kuma muna ƙoƙari mu taimaka musu. (Ro 15:1) Idan wani ya daina bauta wa Jehobah, muna fatan cewa wata rana zai dawo.—Lu 15:17, 18.
KU KALLI BIDIYON NAN KADA MU MANTA YADDA ƘAUNA TAKE—TANA SA ZUCIYA A KOWANE HALI, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:
-
Ta yaya Abner ya yi ta canja ra’ayinsa game da wanda zai goya masa baya?
-
Bayan da Abner ya roƙi gafara, mene ne Dauda ya yi? Mene ne kuma Joab ya yi?
-
Me ya sa ya kamata mu riƙa fatan cewa a yi wa ’yan’uwanmu alheri?