Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Ka Yi Amfani da Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada! don Ka Sa Mutane Su Ba da Gaskiya ga Jehobah da Yesu

Ka Yi Amfani da Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada! don Ka Sa Mutane Su Ba da Gaskiya ga Jehobah da Yesu

Wajibi ne ɗalibanmu su ƙarfafa bangaskiyarsu don su faranta ran Jehobah. (Ibr 11:6) Za mu iya taimaka musu su yi hakan ta wurin amfani da littafin Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! Littafin na ɗauke da muhimman nassosi da bayanai dalla-dalla da tambayoyi masu ratsa zuciya da bidiyoyi masu ƙayatarwa da kuma hotuna masu kyau. Idan mun taimaka wa ɗalibanmu su kasance da halin kirki, kuma su ƙulla dangantaka mai kyau da Jehobah, za su kasance da bangaskiya sosai.​—1Ko 3:​12-15.

Wasu mutane suna ganin cewa zai yi wuya su ƙulla dangantaka mai kyau da Jehobah domin ba sa ganin sa. Saboda haka, muna bukatar mu taimaka musu su san Jehobah kuma su dogara gare shi.

KU KALLI BIDIYON NAN KU TAIMAKA WA ƊALIBANKU SU BA DA GASKIYA GA JEHOBAH DA LITTAFIN “KA JI DAƊIN RAYUWA HAR ABADA!” SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Ta yaya muka san cewa ’yar’uwar ta yi shiri sosai don nazarin?

  • Ta yaya ta yi amfani da tambayoyi masu kyau don ta san ra’ayin ɗalibarta bayan sun karanta Ishaya 41:​10, 13?

  • Ta yaya bidiyo da kuma ayoyin da suka karanta suka ratsa zuciyar ɗalibar?

Mutane da yawa ba su san abin da ya sa Yesu ya ba da ransa ba, ko kuma suna ganin fansar ba za ta amfane su ba. (Ga 2:​20, NWT) Saboda haka, muna bukatar mu taimaka musu su ba da gaskiya ga fansar Yesu.

KU KALLI BIDIYON NAN KU TAIMAKA WA ƊALIBANKU SU BA DA GASKIYA GA YESU DA LITTAFIN “KA JI DAƊIN RAYUWA HAR ABADA!” SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Ta yaya muka san cewa ɗan’uwan ya yi shiri sosai don nazarin?

  • Ta yaya ya yi amfani da bayanin da ke sashen “Ka Bincika” don ya taimaka wa ɗalibin?

  • Me ya sa yin addu’a tare da ɗalibin yake da muhimmanci?