Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Kana Shirye don Lokacin Tashin Hankali?

Kana Shirye don Lokacin Tashin Hankali?

Yayin da muke gab da ƙarshen zamanin nan, tashin hankali, ta’addanci da yaƙe-yaƙe za su ƙaru. (R. Yar 6:4) Ta yaya za mu yi shiri don matsalolin da za mu fuskanta a nan gaba?

  • Ka shirya yadda za ka kasance da aminci: Ka nemi ƙa’idodi da labaran Littafi Mai Tsarki da za su sa ka ƙara dogara ga Jehobah da ƙungiyarsa. Hakan zai taimaka maka ka riƙe aminci. (K. Ma 12:5; jr-E 125-126 sakin layi na 23-24) Yanzu ne ya kamata ka ƙulla dangantaka na kud da kud da ’yan’uwa a ikilisiya.​—1Bi 4:​7, 8

  • Ka shirya abubuwan da za ka yi amfani da su: Ka shirya abin da za ka yi idan ba za ka iya barin gida ba, kuma ka yi ƙoƙari ka sami abubuwan da ka san za ka bukace su a lokacin. Ƙari ga haka, ka yi tunanin hanyar da za ka bi ka gudu idan bukata ta tashi. Ka sake dudduba abubuwan da ke jakar gaggawarka, kuma ka tabbata cewa akwai kuɗi da abubuwan da za ka kāre kanka da su kamar, takunkumin fuska ko safar hannu. Ka kasance da lambar dattawa ko ka san yadda za ka same su, kuma ka tabbata sun san yadda za su same ka.​—Ish 32:2; g17.5-E 3-7

A lokacin tashin hankali, ka ci gaba da yin ibadarka yadda ka saba. (Fib 1:10) Kada ka riƙa ƙaura zuwa wurare dabam-dabam sai dai hakan ya zama dole. (Mt 10:16) Ka samma mutane abinci da wasu abubuwan da kake da su.​—Ro 12:13.

KU KALLI BIDIYON NAN A SHIRYE KAKE IDAN BALA’I TA AUKU? SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Ta yaya Jehobah zai taimaka mana a lokacin bala’i?

  • Waɗanne abubuwa ne za mu iya yi don mu kasance a shirye?

  • Ta yaya za mu iya taimaka ma waɗanda bala’i ya shafa?