Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

“Ƙauna . . . Ba Ta Yin Girman Kai”

“Ƙauna . . . Ba Ta Yin Girman Kai”

Ƙauna tana taimaka mana mu zama masu tawali’u. (1Ko 13:4) Idan muna ƙaunar ’yan’uwanmu, ba za mu ɗauki kanmu da muhimmanci fiye da su ba. Muna mai da hankali ga halaye masu kyau na ’yan’uwanmu kuma muna yin amfani da baiwarmu don mu taimaka musu. (Fib 2:​3, 4) Idan mun ci gaba da nuna irin wannan ƙaunar, Jehobah zai yi amfani da mu don ya cim ma nufinsa.

KU KALLI BIDIYON NAN KADA MU MANTA YADDA ƘAUNA TAKE​—BA TA YIN GIRMAN KAI, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Waɗanne irin baiwa ne Absalom yake da su?

  • Ta yaya ya yi amfani da baiwarsa a hanyar da ba ta dace ba?

  • Ta yaya za mu guji zama masu girman kai?​—Ga 5:26