30 ga Mayu–5 ga Yuni
2 SAMA’ILA 7-8
Waƙa ta 22 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 1)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Jehobah Ya Yi wa Dauda Alkawari”: (minti 10)
Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah: (minti 10)
2Sam 8:2—Wane annabci ne Dauda ya cika sa’ad da ya ci mutanen Mowab da yaƙi? (it-2-E 206 sakin layi na 2)
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu game da Jehobah da wa’azi da dai sauransu?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4) 2Sam 7:1-17 (th darasi na 5)
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Haɗuwa ta Fari: (minti 3) Ka bi bayanin da ke yadda za mu yi wa’azi, kuma ka ambata yadda hakan yake da alaƙa da wani abin da ke faruwa a yankinku. Ka ba wa maigidan mujallar da ta tattauna batun da ya tayar. (th darasi na 13)
Komawa Ziyara: (minti 4) Ka soma da bin bayanin da ke yadda za mu yi wa’azi, kuma ka ambata yadda hakan yake da alaƙa da wani abin da ke faruwa a yankinku. Ka bayyana wa mutumin yadda muke yin nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane kyauta kuma ka ba shi katin jw.org. (th darasi na 18)
Nazarin Littafi Mai Tsarki: (minti 5) lff taƙaitawa, bita da maƙasudi na darasi na 04 (th darasi na 8)
RAYUWAR KIRISTA
Bukatun Ikilisiya: (minti 10)
“Ka Yi Amfani da Abubuwan da Ke Faruwa a Wa’azi”: (minti 5) Tattaunawa.
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) lff darasi na 06
Kammalawa (minti 3)
Sabuwar Waƙa na Taron Yanki na 2022 da Addu’a