30 ga Mayu–5 ga Yuni
Ka Yi Amfani da Abubuwan da Ke Faruwa a Wa’azi
Yesu ya yi amfani da abubuwan da ke faruwa don ya koya wa mutane darussa sa’ad da yake wa’azi. (Lu 13:1-5) Kai ma za ka iya yin amfani da abubuwan da ke faruwa don ka sa mutane su so jin wa’azi. Za ka iya ambata yadda abubuwa suke tsada sosai ko bala’i ko tashin hankali da dai sauransu. Bayan hakan, za ka iya yi wa mutumin tambaya cewa: “Kana ganin za mu taɓa ganin ƙarshen . . . ?” ko kuma “Mene ne kake ganin zai iya magance . . . ?” Sai ka karanta wa mutumin wata ayar da ta yi magana a kan batun. Idan mutumin yana so ku ci gaba da tattaunawa, ka nuna masa bidiyo ko wani littafi da ke Kayan Aiki don Koyarwa. Yayin da muke iya ƙoƙarinmu mu ratsa zukatan mutane da ke yankinmu, bari mu yi hakan “saboda labari mai daɗi.”—1Ko 9:22, 23.
Waɗanne batutuwa ne kake ganin mutane a yankinku za su so tattaunawa?