Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Ka Riƙa Ganin Kanka Kamar Yadda Jehobah Yake Ganinka

Ka Riƙa Ganin Kanka Kamar Yadda Jehobah Yake Ganinka

Littafi Mai Tsarki ya ce, Jehobah “yakan ji daɗin mutanensa.” (Za 149:4) Duk da cewa mu ajizai ne, yana ganin halayenmu masu kyau da kuma abin da za mu iya yi a nan gaba. A wasu lokuta, yana da wuya mu kasance da raꞌayin da ya dace game da kanmu. Za mu iya ganin kamar ba mu da amfani domin abin da wasu suka taɓa yi mana. Ƙari ga haka, idan mun mai da hankali a kan kurakuranmu, za mu iya yin shakka cewa Jehobah yana ƙaunarmu da gaske. Mene ne zai taimaka mana idan muka soma jin hakan?

Ku tuna cewa Jehobah yana iya ganin abin da mutane ba za su iya ba. (1Sam 16:7) Hakan yana nufin cewa ya san mu fiye da yadda muka san kanmu. Abin farin cikin shi ne, Littafi Mai Tsarki zai taimaka mana mu san raꞌayin Jehobah game da mu. Za mu fahimci hakan ta wajen karanta labaran Littafi Mai Tsarki da suka nuna yadda Jehobah yake ƙaunar masu bauta masa.

KU KALLI BIDIYON NAN KA SA TUNANINKA YA JITU DA RAꞌAYIN JEHOBAH, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Mene ne misalin mai yin tsere da mahaifinsa ya koya mana game da yadda Jehobah yake ɗaukan mu?

  • Idan mutum ya yi zunubi mai tsanani kuma ya yi ƙoƙarin gyara dangantakarsa da Jehobah, ta yaya zai tabbatar wa kansa cewa Jehobah ya gafarta masa?​—1Yo 3:​19, 20

  • Ta yaya ɗanꞌuwan ya amfana saꞌad da ya karanta kuma ya yi tunani a kan labarin Dauda da na Jehoshafat?