Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Ka Kāre Kanka Daga ꞌYan Ridda

Ka Kāre Kanka Daga ꞌYan Ridda

Shaiɗan da mabiyansa suna yawan gauraya ƙarya da gaskiya don su sa mu yi sanyin gwiwa. (2Ko 11:3) Alal misali, Assuriyawa sun yi amfani da rabin gaskiya da kuma ƙarya don su sa bayin Jehobah sanyin gwiwa. (2Tar 32:​10-15) ꞌYan ridda ma suna hakan a yau. Me za mu yi idan muka ga koyarwar ꞌyan ridda? Mu ɗauke su a matsayin guba! Wajibi ne mu guji karantawa ko amsa musu ko kuma gaya wa wasu game da shi. Ku riƙa saurin gane bayanan da suke sa mutum ya riƙa shakka game da Jehobah da ƙungiyarsa kuma ku guje su!​—Ya 3, 4.

KU KALLI BIDIYON NAN “KU DAGE SOSAI KU KIYAYE BANGASKIYARKU”!​—GAJEREN BIDIYO, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Me ya sa ya kamata mu riƙa mai da hankali saꞌad da muke amfani da dandalin sada zumunta?

  • Ta yaya za mu bi shawarar da ke Romawa 16:17?