RAYUWAR KIRISTA
Kuna Saurarar Littafi Mai Tsarki na Sauti?
Mene ne Littafi Mai Tsarki na Sauti? Yana nufin sautin Littafi Mai Tsarki na juyin New World Translation. Ana fitar da shi a hankali a hankali a harsuna da yawa. Abu na musamman da ke sautin shi ne, kowane mutum da muryarsa dabam a sautin. Ana karanta kalmomin yadda za su nuna kamar mutanen ne suke magana kuma hakan zai sa a fahimci saƙon da ke Littafi Mai Tsarki da kyau.
Ta yaya wasu mutane suke amfana daga sautin? Mutane da yawa da suke saurarar sautin suna jin daɗin yadda yake sa su ji kamar suna wurin saꞌad da abubuwan suke faruwa. Da yake kowane mutum da muryarsa dabam a sautin, hakan yana sa a ƙara fahimtar abin da ke Littafi Mai Tsarki. (K. Ma 4:5) Mutane da yawa da suke saurarar sautin sun ce yana kwantar musu da hankali in suna cikin damuwa.—Za 94:19.
Sauraron Kalmar Allah yana taimaka wa mutum a rayuwa. (2Tar 34:19-21) Idan akwai sautin Littafi Mai Tsarki gabaki ɗaya ko wani ɓangare a yarenku, zai dace ka riƙa saurarawa kullum.
KU KALLI BIDIYON NAN YADDA AKE SHIRYA SAUTIN LITTAFI MAI TSARKI—GAJEREN BIDIYO, SAI KU AMSA TAMBAYA TA GABA:
Mene ne ya burge ka game da yadda ake shirya sautin Littafi Mai Tsarki?