Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Ku Riƙa Farin Cikin Soma Tattaunawa da Mutane

Ku Riƙa Farin Cikin Soma Tattaunawa da Mutane

Tattaunawa da mutane saꞌad da muka sami zarafi yana sa mutum farin ciki sosai kuma hakan hanya ce mai kyau na yin waꞌazi. Duk da haka, muna iya jin tsoron soma tattaunawa da mutane idan muka mai hankali ainun ga yadda za mu gabatar da wani Nassi. Maimakon ku riƙa yawan damuwa da abin da za ku faɗa, ku mai da hankali wajen nuna kun damu da mutanen. (Mt 22:39; Fib 2:4) Idan kuka samu zarafin yin waꞌazi, kuna da kayan aiki da yawa da za su taimaka muku.

Ta yaya waɗannan abubuwan da aka ambata a ƙasa, za su taimaka muku ku yi waꞌazi a kan wani batu da ya taso?

KU KALLI BIDIYON NAN “KARFE YAKAN WASA KARFE”​—SOMA TATTAUNAWA, SAI KU AMSA TAMBAYA TA GABA:

Waɗanne abubuwa uku ne za su taimaka mana mu inganta yadda muke tattaunawa da mutane?