Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Jehobah Ne “Baban Marayu”

Jehobah Ne “Baban Marayu”

A kowace shekara, matasa da yawa suna zama abokan Jehobah. (Za 110:3) Jehobah ya damu da kowannenku. Ya san matsalolin da kuke fuskanta kuma ya yi alkawari zai taimaka muku ku bauta masa. Idan mahaifinka ko mahaifiyarka ce kaɗai ta rene ka, ka tuna cewa Jehobah ne “baban marayu.” (Za 68:5) Da taimakon Jehobah za ka yi nasara a duk yanayin da ka sami kanka a ciki.​—1Bi 5:10.

KU KALLI BIDIYON NAN SUNA DAGEWA WAJEN KIYAYE BANGASKIYARSU​—WADANDA MAHAIFINSU NE KO MAHAIFIYARSU CE KADAI TAKE KOYA MUSU GAME DA JEHOBAH, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Mene ne kuka koya daga labarin Tammy da Charles da kuma Jimmy?

  • Ta yaya abin da ke Zabura 27:10 zai ƙarfafa waɗanda mahaifinsu ko mahaifiyarsu ce kaɗai ta rene su?