Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Kuna Shirye don Faɗuwar Tattalin Arziki?

Kuna Shirye don Faɗuwar Tattalin Arziki?

Ba ma mamaki saꞌad da abubuwan da ke faruwa a duniya suka taɓarɓare tattalin arziki. Me ya sa? Domin muna rayuwa a ƙarshen kwanaki na ƙarshe kuma Littafi Mai Tsarki ya gargaɗe mu kada mu dogara ga “arziki marar tabbata.” (1Ti 6:17; 2Ti 3:1) Mene ne abin da ya faru da Sarki Jehoshafat ya koya mana game da kasancewa a shirye don faɗuwar tattalin arziki?

Jehoshafat ya dogara ga Jehobah saꞌad da maƙiyansa suka yi barazanar yaƙi da shi. (2Tar 20:​9-12) Ƙari ga haka, ya yi shirye-shirye ta wajen gina katanga da kuma kafa barikin sojoji da yawa. (2Tar 17:​1, 2, 12, 13) Kamar Jehoshafat, zai dace mu dogara ga Jehobah kuma mu yi shirye-shiryen fuskantar yanayoyi masu wuya.

KU KALLI BIDIYON NAN A SHIRYE KAKE IDAN BALAꞌI TA AUKU? SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Mene ne za mu iya yi don mu yi shiri kafin balaꞌi ta auku?

  • Ta yaya za mu kasance a shirye don mu taimaka wa mutane?