17-23 ga Yuni
ZABURA 51-53
Waƙa ta 89 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)
1. Me Za Ku Iya Yi don Ku Guji Yin Kuskure Mai Tsanani?
(minti 10)
Kada ku yi tunani cewa ba za ku iya yin kuskure ba, domin yana da sauƙi ꞌyan Adam su yi abin da bai da kyau (Za 51:5; 2Ko 11:3)
Ku ci gaba da yin abubuwan da za su taimaka muku ku kusaci Jehobah (Za 51:6; w19.01 15 sakin layi na 4-5)
Ku riƙa guje wa tunani da kuma shaꞌawar banza (Za 51:10-12; w15 6/15 14 sakin layi na 5-6)
2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah
(minti 10)
-
Za 52:2-4—Ta yaya ayoyin nan sun kwatanta ayyukan Dowek? (it-1-E 644)
-
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu?
3. Karatun Littafi Mai Tsarki
(minti 4) Za 51:1-19 (th darasi na 12)
4. Fara Magana da Mutane
(minti 2) WAꞌAZI A INDA JAMAꞌA SUKE. (lmd darasi na 7 batu na 3)
5. Fara Magana da Mutane
(minti 2) WAꞌAZI GIDA-GIDA. (lmd darasi na 4 batu na 4)
6. Komawa Ziyara
(minti 3) SAꞌAD DA KAKE AYYUKA NA YAU DA KULLUM. Ka gaya wa mutumin sunan Allah. (lmd darasi na 9 batu na 5)
7. Almajirtarwa
Waƙa ta 115
8. Ta Yaya Za Mu Gyara Kurakuranmu?
(minti 15) Tattaunawa.
Dukanmu muna yin kuskure duk da ƙoƙarin da muke yi. (1Yo 1:8) Idan muka yi kuskure, ba zai dace mu bar kunya ko kuma tsoro ya hana mu neman gafara da taimako daga wurin Jehobah ba. (1Yo 1:9) Yin Adduꞌa ga Jehobah shi ne abu na farko da ya kamata mu yi don mu yi gyara kuskuren da muka yi.
Karanta Zabura 51:1, 2, 17. Sai ka tambayi masu sauraro:
-
Ta yaya kalmomin Dauda za su taimaka mana mu nemi taimakon Jehobah idan muka yi kuskure mai tsanani?
Ku kalli BIDIYON Rayuwar Matasa—Ta Yaya Zan Gyara Kurakuraina? Sai ka tambayi masu sauraro:
-
Waɗanne abubuwa ne suka sa Thalila da José su yi kuskure?
-
Mene ne suka yi don su gyara kurakuransu?
-
Ta yaya suka amfana daga yin hakan?
9. Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya
(minti 30) kr babi na 12 sakin layi na 16-23 akwatin da ke shafi na 125 da 128 da 129