Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

20-26 ga Mayu

ZABURA 40-41

20-26 ga Mayu

Waƙa ta 102 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

1. Me Ya Sa Muke Taimaka Wa Mutane?

(minti 10)

Taimaka wa mutane yana sa mu yi farin ciki (Za 41:1; w18.08 22 sakin layi na 16-18)

Jehobah yana taimaka ma waɗanda suke taimaka wa mutane (Za 41:​2-4; w15 12/15 24 sakin layi na 7)

Muna ɗaukaka Jehobah idan muna taimaka wa mutane (Za 41:13; K. Ma 14:31; w17.09 12 sakin layi na 17)

KA TAMBAYI KANKA, ‘Shin, akwai wani ko wata a ikilisiyarmu da take bukatar taimako game da yadda ake amfani da manhajar JW Library?’

2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah

(minti 10)

  • Za 40:​5-10—Mene ne muka koya daga adduꞌar Dauda game da amincewa da matsayin Jehobah na Maɗaukaki? (it-2-E 16)

  • A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu?

3. Karatun Littafi Mai Tsarki

(minti 4) Za 40:​1-17 (th darasi na 12)

KA YI WAꞌAZI DA ƘWAZO

4. Fara Magana da Mutane

(minti 3) SAꞌAD DA KAKE AYYUKA NA YAU DA KULLUM. Ka soma tattaunawa da wani da yake farin ciki. (lmd darasi na 2 batu na 3)

5. Fara Magana da Mutane

(minti 4) SAꞌAD DA KAKE AYYUKA NA YAU DA KULLUM. Ka soma tattaunawa da wani da yake baƙin ciki. (lmd darasi na 3 batu na 5)

6. Almajirtarwa

(minti 5) lff darasi na 14 batu na 6. Ka tattauna wani batu daga talifin nan “Mu Yabi Jehobah a Cikin Ikilisiya” da ke sashen “Ka Bincika” da ɗalibin da yake jinkirin halartar taro. (th darasi na 19)

RAYUWAR KIRISTA

Waƙa ta 138

7. Ku Riƙa YI Wa Tsofaffi Alheri

(minti 15) Tattaunawa.

Jehobah yana daraja dukan aikin da ꞌyanꞌuwanmu tsofaffi suke yi a ikilisiya, haka mu ma. (Ibr 6:10) Sun yi shekaru da yawa suna koyar da horar da kuma ƙarfafa sauran ꞌyanꞌuwa. Mai yiwuwa ka tuna da yadda suka taimaka maka. Ta yaya za ka nuna godiya don dukan abubuwan da suka yi da kuma suke yi a ikilisiya?

Ku kalli BIDIYON ‘Mu Kyautata Wa ’Yan’uwanmu.’ Sai ka tambayi masu sauraro:

  • Mene ne Ji-Hoon ya koya daga Ɗanꞌuwa Ho-jin Kang?

  • Mene ne ke burge ka game da tsofaffi a ikilisiyarku?

  • Wane darasi ne muka koya daga labarin Basamariye?

  • Me ya sa kake gani ya dace da Ji-Hoon ya kira wasu ꞌyanꞌuwa saꞌad da ya je ya taimaka wa Ɗanꞌuwa Ho-jin Kang?

Idan mun yi tunani game da bukatun tsofaffi a ikilisiyarmu, za mu nemi zarafi mu taimaka musu. Idan ka ga cewa suna da bukata, ka ɗauki mataki don ka taimaka.—Yak 2:​15, 16

Karanta Galatiyawa 6:10. Sai ka tambayi masu sauraro:

  • A waɗanne hanyoyi ne za ku iya “yi wa tsofaffi alheri” a ikilisiyarku?

8. Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya

Kammalawa (minti 3) | Waƙa ta 8 da Adduꞌa