24-30 ga Yuni
ZABURA 54-56
Waƙa ta 48 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)
1. Allah Yana Tare da Kai
(minti 10)
Kamar Dauda, ku dogara ga Jehobah a duk lokacin da kuke jin tsoro (Za 56:1-4; w06 8/1 18 sakin layi na 10-11)
Jehobah yana farin ciki don yadda kuke jimrewa kuma zai taimaka muku (Za 56:8; cl 243 sakin layi na 9)
Jehobah yana tare da ku. Ba zai bar wani abu ya jawo muku lahani na dindindin ba (Za 56:9-13; Ro 8:36-39; w22.06 18 sakin layi na 16-17)
2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah
(minti 10)
-
Za 55:12, 13—Shin, Jehobah ya riga ya shirya cewa Yahuda ne zai bashe Yesu? (it-1-E 857-858)
-
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu?
3. Karatun Littafi Mai Tsarki
(minti 4) Za 55:1-23 (th darasi na 10)
4. Fara Magana da Mutane
(minti 3) WAꞌAZI A INDA JAMAꞌA SUKE. Ka gaya wa mutumin yadda muke yin nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane kyauta kuma ka ba shi katin nazarin Littafi Mai Tsarki. (th darasi na 11)
5. Komawa Ziyara
(minti 4) SAꞌAD DA KAKE AYYUKA NA YAU DA KULLUM. (lmd darasi na 7 batu na 4)
6. Jawabi
(minti 5) w23.01 29-30 sakin layi na 12-14—Jigo: Ƙaunarmu ga Kristi Na Sa Mu Kasance da Ƙarfin Zuciya. Ku duba hoto. (th darasi na 9)
Waƙa ta 153
7. Zai Yiwu Mu Yi Farin Ciki ko Da . . . Za A Kashe Mu
(minti 5) Tattaunawa.
Ku kalli BIDIYON. Sai ka tambayi masu sauraro:
-
Mene ne ka koya daga labarin Ɗanꞌuwa Dugbe da zai taimaka maka a lokacin da kake jin tsoro?
8. Abubuwan da Ƙungiyarmu Ta Cim Ma na watan Yuni
(minti 10) Ku kalli BIDIYON.