Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

27 ga Mayu–2 ga Yuni

ZABURA 42-44

27 ga Mayu–2 ga Yuni

Waƙa ta 86 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

1. Ku Riƙa Bin Umurnin Jehobah Don Ku Amfana

(minti 10)

Zai dace ku riƙa bauta wa Jehobah tare da sauran ꞌyanꞌuwa a wuraren ibadarmu (Za 42:​4, 5; w06 7/1 19 sakin layi na 1)

Ku riƙa yin adduꞌa kafin ku yi nazarin Kalmar Allah (Za 42:8; w12 1/15 15 sakin layi na 2)

Bari Littafi Mai Tsarki ya ja-goranci duk abin da kuke yi a rayuwa (Za 43:3)

Umurnin Jehobah suna taimaka mana mu jimre matsaloli kuma mu ci gaba da riƙe alkawarinmu na bauta masa har abada.—1Bi 5:10; w16.09 5 sakin layi na 11-12.

2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah

(minti 10)

  • Za 44:19—Mene ne maꞌanar furucin nan “a hannun karnukan daji”? (it-1 E 1242)

  • A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu?

3. Karatun Littafi Mai Tsarki

(minti 4) Za 44:​1-26 (th darasi na 11)

KA YI WAꞌAZI DA ƘWAZO

4. Fara Magana da Mutane

(minti 4) WAꞌAZI GIDA-GIDA. Ka tambayi mutumin ko zai so a yi nazari da shi. (lmd darasi na 5 batu na 5)

5. Komawa Ziyara

(minti 5) WAꞌAZI GIDA-GIDA. Ka gayyaci mutumin zuwa jawabi ga jamaꞌa da za a yi a taro. Ka gabatar kuma ku tattauna (amma kar ka kunna) bidiyon nan Me Ake Yi a Majami’ar Mulki? (lmd darasi na 7 batu na 5)

6. Jawabi

(minti 3) lmd ƙarin bayanai na 1 batu na 4—Jigo: Kowa Zai Sami Cikakken Lafiya. (th darasi na 2)

RAYUWAR KIRISTA

Waƙa ta 21

7. Ka Yanke Shawara Mai Kyau Game da AIki da Kuma Makaranta

(minti 15) Tattaunawa.

Matasa kuna tunani a kan abin da za ku yi bayan kun gama makarantar sakandare? Wataƙila akwai aikin da za ku so ku yi da zai ba ku damar yin hidimar majagaba. Ko kuma kuna tunanin zuwa makarantun da za su sa ku sami ƙwarewar ko lasisi ko difuloma, da zai taimaka muku ku sami irin aikin. Wannan lokaci ne mai muhimmanci a rayuwarku. Ban da haka, wataƙila zai yi muku wuya ku zaɓi aikin da za ku yi don akwai ayyuka da dama, ko kuma ana matsa muku ku yi aikin da zai burge mutane. Mene ne zai taimaka muku ku yanke shawarar da ta dace?

Karanta Matiyu 6:​32, 33. Sai ka tambayi masu sauraro:

  • Me ya sa ya kamata mu kasance da maƙasudi kafin mu yanke shawarwarin da suke da muhimmanci game da aiki da kuma makaranta?

  • Ta yaya iyaye za su iya taimaka wa yaransu su bi abin da ke Matiyu 6:​32, 33?—Za 78:​4-7

Ku yi hankali kada neman kuɗi ko kuma neman suna ya shafi shawarar da za ku yanke. (1Yo 2:​15, 17) Ku tuna cewa zama da arziki sosai kawai ma zai iya sa ya zama da wuya mutum ya ji waꞌazin Mulki. (Lu 18:​24-27) Neman arziki ido rufe, zai iya hana mutum ƙarfafa dangantakarsa da Allah.—Mt 6:24; Mk 8:36.

Ku kalli BIDIYON Kada Ku Dogara ga Abubuwan da Ba Za Su Dawwama Ba!—Arziki. Sai ka tambayi masu sauraro:

  •   Ta yaya abin da ke Karin Magana 23:​4, 5 zai taimaka maka ka yanke shawara mai kyau?

8. Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya

Kammalawa (minti 3) | Waƙa ta 47 da Adduꞌa