3-9 ga Yuni
ZABURA 45-47
Waƙa ta 27 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)
1. Waƙar da Aka Yi Game da Auren Wani Sarki
(minti 10)
A Zabura 45 an kwatanta yadda za a yi auren Sarkin Mulkin Allah (Za 45:1, 13, 14; w14 2/15 9-10 sakin layi na 8-9)
Za a yi auren nan bayan Armageddon (Za 45:3, 4; w22.05 17 sakin layi na 10-12)
Dukan ꞌyan Adam za su sami albarka don auren nan da za a yi (Za 46:8-11; it-2-E 1169)
KA TAMBAYI KANKA, ‘Ina marmarin gaya wa mutane game da Sarkinmu Yesu Kristi?’—Za 45:1.
2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah
(minti 10)
-
Za 45:16—Mene ne ayar nan ta koya mana game da yadda rayuwa za ta kasance a Aljanna? (w17.04 11 sakin layi na 9)
-
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu?
3. Karatun Littafi Mai Tsarki
(minti 4) Za 45:1-17 (th darasi na 5)
4. Fara Magana da Mutane
(minti 3) SAꞌAD DA KAKE AYYUKA NA YAU DA KULLUM. (lmd darasi na 1 batu na 3)
5. Jawabi
(minti 5) ijwbv 26—Jigo: Mene ne Abin da Ke Zabura 46:10 Yake Nufi? (th darasi na 18)
6. Ka Bayyana Imaninka
(minti 4) Gwaji. g 12/10 22-23—Jigo: Mene ne Raꞌayinka Game da Luwaɗi? (lmd darasi na 6 batu na 5)
Waƙa ta 131
7. Ku Ci-gaba da Nuna Ƙauna a Aurenku
(minti 10) Tattaunawa.
Bikin aure abin farin ciki ne. (Za 45:13-15) A yawancin lokuta, ranar bikin aure yakan zama ɗaya daga cikin ranakun da ya fi sa maꞌaurata farin ciki. Amma mene ne maꞌauratan za su yi don su ci gaba da jin daɗin aurensu muddin ransu?—M. Wa 9:9.
Idan suna so su ji daɗin aurensu, wajibi ne su ci gaba da ƙaunar juna. Maꞌaurata suna bukata su yi koyi da Ishaku da Rifkatu. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa bayan sun yi shekaru 30 da aure, suna nan suna nuna wa juna ƙauna. (Fa 26:8) Mene ne zai taimaka wa maꞌaurata su riƙa nuna irin wannan ƙaunar?
Ku kalli BIDIYON Abin da Zai Sa Maꞌaurata Farin Ciki: Ku Nuna Kauna. Sai ka tambayi masu sauraro:
-
Mene ne zai iya sa maꞌaurata su rage ƙaunar juna?
-
Mene ne maꞌaurata za su riƙa yi wa juna da zai nuna cewa suna ƙaunar juna kuma sun damu da juna?—A. M 20:35
8. Bukatun Ikilisiya
(minti 5)