6-12 ga Mayu
ZABURA 36-37
Waƙa ta 87 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)
1. “Kada Ka Damu Saboda Mugaye”
(minti 10)
Mugaye suna sa mu sha wahala (Za 36:1-4; w17.04 10 sakin layi na 4)
Idan muka ci gaba da jin haushin “mugaye” hakan zai jawo mana matsala (Za 37:1, 7, 8; w22.06 10 sakin layi na 10)
Idan muka gaskata da alkawuran Jehobah, za mu sami kwanciyar hankali (Za 37:10, 11; w03 12/1 25 sakin layi na 20)
KA TAMBAYI KANKA, ‘Shin, ina yawan mai da hankali ga munanan abubuwan da ake faɗa a labarai?’
2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah
(minti 10)
-
Za 36:6—Mene ne marubucin zaburar nan yake nufi saꞌad da ya ce adalcin Jehobah yana kama da “babban tudu”? (it-2-E 445)
-
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu?
3. Karatun Littafi Mai Tsarki
(minti 4) Za 37:1-26 (th darasi na 10)
4. Fara Magana da Mutane
(minti 3) WAꞌAZI GIDA-GIDA. (lmd darasi na 1 batu na 5)
5. Komawa Ziyara
(minti 4) SAꞌAD DA KAKE AYYUKA NA YAU DA KULLUM. Ka nuna wa wani mutum da ya taɓa ƙin yin nazari yadda muke gudanar da nazari. (lmd darasi na 9 batu na 4)
6. Jawabi
(minti 5) ijwbv 45-E—Jigo: Mene ne Abin da Ke Zabura 37:4 Yake Nufi? (th darasi na 13)
Waƙa ta 33
7. Kuna Shirye don “Lokacin Wahala”?
(minti 15) Tattaunawa.
Balaꞌoꞌin da suke faruwa suna sa ꞌyanꞌuwanmu a fadin duniya su rasa mutanensu da kuma kayayyakinsu. (Za 9:9, 10) Abin baƙin ciki shi ne, za mu iya shan “wahala” a kowane lokaci, don haka muna bukata mu kasance a shirye don iri lokacin nan.
Ban da kasancewa a shirye, a mene ne zai taimaka mana mu jimre idan balaꞌi ya auku?
-
Ku shirya zuciyarku: Zai dace mu gaya wa kanmu gaskiya cewa balaꞌoꞌi suna faruwa, kuma mu yi tunanin abin da za mu iya yi idan ya faru. Bai kamata mu so kayan da muka mallaka fiye da kima ba. Hakan zai taimaka mana mu kasance da hikima wajen kāre ranmu da na wasu, maimakon abubuwan da muka mallaka. (Fa 19:16; Za 36:9) Ƙari ga haka, idan ba ma son kayan da muka mallaka fiye da kima, hakan zai taimaka mana mu jimre ko da mun rasa kayan a lokacin balaꞌi.—Za 37:19
-
Ku ƙarfafa dangantakarku da Jehobah: Mu gaskata cewa Jehobah zai iya taimaka mana kuma yana so ya yi hakan. (Za 37:18) Kafin balaꞌi ya auku, zai dace mu riƙa tuna cewa Jehobah zai ja-goranci kuma ya taimaka wa bayinsa ko da sun tsira da ransu ne kawai.—Irm 45:5; Za 37:23, 24
Idan muka kasance da tabbaci cewa Jehobah zai cika alkawuransa, hakan ya nuna cewa ‘shi ne wurin ɓuyanmu a lokacin wahala.’—Za 37:39.
Ku kalli BIDIYON A Shirye Kake Idan Balaꞌi ta Auku? Sai ka tambayi masu sauraro:
-
Ta yaya Jehobah yake taimaka mana a lokacin balaꞌi?
-
Mene ne za mu iya yi don mu kasance a shirye?
-
Ta yaya za mu iya taimaka wa waɗanda balaꞌi ya shafa?
8. Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya
(minti 30) kr babi na 10 sakin layi na 12-19, akwatin da ke shafi na 105 (na dama) da 107
Kammalawa (minti 3) |
a Ka duba Awake! Na 5 2017, shafi na 4-6.