RAYUWAR KIRISTA
Yadda Za a Yi Amfani da Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
Littattafan nan Me Za Mu Koya da Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? iri ɗaya ne. Muna amfani da dukansu a wa’azi kuma yadda aka tsara su iri ɗaya ne. Amma Me Za Mu Koya yana da sauƙin karatu da kuma fahimta. An wallafa shi don mutanen da ba za su iya fahimtar Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? ba. An saka ƙarin bayani a Me Za Mu Koya maimakon rataye. Ƙarin bayanin ya bayyana wasu batutuwa da ke cikin babin a hanyar da za a fahimce su da sauƙi. Babu tambayoyi a farkon babin ko kuma akwatin bita a ƙarshen babin. Amma, an kammala kowane babi da taƙaita wasu muhimman darussan da aka bayyana a babin. Za mu iya ba da littafin Me Za Mu Koya yadda muke ba da Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? ko da ba shi ake rarraba a watan ba. Ta yaya za mu yi amfani da littafin Me Za Mu Koya wajen yin nazari da mutane?
TAƘAITAWA: Yawancin mutane za su fi amfana daga yadda muke yin nazari da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?, wato yadda muke karanta sakin layi da kuma yin tambaya. Amma idan mutumin ba ya jin yaren sosai ko kuma bai iya karatu ba fa? Ta yaya za a iya taimaka masa? Za a iya yin amfani da littafin nan Me Za Mu Koya. Idan hakan ne, za a iya amfani da taƙaitawar don yin nazarin kuma bayan an gama, a ce wa ɗalibin ya karanta sakin layin a nasa lokaci. Za a iya koyar da kowane darasi cikin minti 15. Da yake taƙaitawar ba ta ɗauke da cikakken bayanai da ke babin, zai dace malamin ya yi la’akari da yanayin ɗalibinsa kuma ya yi shiri da kyau. Amma idan malamin ya yi amfani da sakin layin wajen yin nazarin, zai dace ya yi amfani da taƙaitawar don bita.
ƘARIN BAYANAI: An jera kalmomi da kuma batutuwan da ke ƙarin bayanin ɗaya bayan ɗaya yadda yake a babin. Mai gudanar da nazarin zai iya tsai da shawarar tattauna ƙarin bayani da ke littafin Me Za Mu Koya sa’ad da yake nazari.