Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | MAI-WA’AZI 7-12

“Ka Tuna da Mahaliccinka . . . a Cikin Kwanakin Kuruciyarka”

“Ka Tuna da Mahaliccinka . . . a Cikin Kwanakin Kuruciyarka”

Ka tuna da Mahaliccinka ta wajen yin amfani da ƙwarewarka don bauta masa sa’ad da kake matashi

12:1, 13

  • Matasa da yawa suna iya bi da ƙalubale da kuma aiki mai wuya domin suna da koshin lafiya da ƙarfi

  • Ya kamata matasa su yi amfani da lokacinsu da kuma ƙarfinsu a hidimar Jehobah kafin su tsufa kuma su ƙasa yin hakan

Sulemanu ya yi amfani da fasahar magana wajen kwatanta lokacin tsufa

12:2-7

  • Aya ta 3: ‘Yan matan da ‘suke leƙa ta cikin sakata sun duhunta’

    Rashin gani sosai

  • Aya ta 4: ‘Mata masu-rairawa sun yi shiru’

    Rashin ji sosai

  • Aya ta 5: ‘Ya’yan itace “sun lalace”

    Raguwar marmarin abinci