Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | 2 YOHANNA 1-13; 3 YOHANNA 1-14YAHUDA 1-25

Dole Mu Dāge Sosai Mu Kiyaye Bangaskiyarmu

Dole Mu Dāge Sosai Mu Kiyaye Bangaskiyarmu

Yahuda 3

Yesu ya ce: “Ku yi ƙoƙari ku shiga ta ƙaramar ƙofa.” (Lu 13:24) Kalaman Yesu sun nuna cewa za mu yi kokawa sosai ko kuma mu dāge kafin Allah ya amince da mu. Yahuda ɗan’uwan Yesu ma an hore shi ya yi magana kamar haka, ya ce: “Ku dāge sosai ku kiyaye bangaskiyarku.” Dole ne mu yi iya ƙoƙarinmu kafin mu yi abubuwa na gaba:

  • Mu ƙi yin lalata.​—Yahuda 6, 7

  • Mu yi ma waɗanda suke ja-gora a ikilisiya biyayya.​—Yahuda 8, 9

  • Mu ƙarfafa ‘bangaskiyarmun nan mafi tsarki,’ wato, koyarwarmu ta Kirista.​—Yahuda 20, 21