Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | RU’UYAR DA AKA YI WA YOHANNA 1-3

“Na San Ayyukanku”

“Na San Ayyukanku”

1:20; 2:​1, 2

  • “Taurari bakwai”: Suna nufin dattawa waɗanda shafaffu ne da kuma sauran dattawan

  • ‘A hannun damar [Yesu]’: Yesu ne yake iko da dattawa kuma shi yake musu ja-gora. Idan wani dattijo yana bukatar gyara, Yesu zai sa a yi masa hakan a daidai lokaci da kuma hanyar da ta dace

  • “Sandunan zinariya guda bakwai masu riƙe fitilu”: Suna nufin ikilisiyoyin Kirista. Kamar yadda fitilar da ke cikin mazauni take haskaka ko’ina, haka ma ’yan’uwa da ke cikin ikilisiyoyi suke haskaka ko nuna gaskiyar Kalmar Allah. (Mt 5:14) Yesu yana “tafiya” tsakanin waɗannan sandunan fitilu, wato yana yi wa ikilisiyoyin ja-gora