Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | RU’UYAR DA AKA YI WA YOHANNA 4-6

Fitowar Mahaya Hudu

Fitowar Mahaya Hudu

6:​2, 4-6, 8

Yesu “ya ƙara cin nasara” ta wajen yin yaƙi da Shaiɗan da aljanunsa a sama kuma ya jefo su nan duniya. Ba za su iya sake komawa sama ba. Yesu ya ci gaba da yin nasara a madadin bayinsa ta wajen taimaka musu da kuma kāre su a wannan kwanakin ƙarshe. Zai gama “cin nasara” sa’ad da ya halaka sauran mahaya ukun a yaƙin Armageddon. Bayan haka, zai mai da duniyar nan aljanna.