23-29 ga Nuwamba
LITTAFIN FIRISTOCI 6-7
Waƙa ta 46 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 1)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Nuna Godiya”: (minti 10)
L.Fi 7:11, 12—Ɗaya daga cikin hadaya ta gyaran zumunci ita ce hadayar da ake bayarwa da yardar rai don nuna godiya (w19.11 22 sakin layi na 9)
L.Fi 7:13-15—Wanda yana ba da hadaya ta gyaran zumunci a alamance shi da iyalinsa suna cin abinci da Jehobah kuma hakan yana nuna cewa suna da dangantaka mai kyau da shi (w00 9/1 7 sakin layi na 15)
L.Fi 7:20—Waɗanda suke da tsarki ne kawai Jehobah zai amince da hadayarsu ta gyaran zumunci (w00 9/1 11 sakin layi na 8)
Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 10)
L.Fi 6:13—Wane ra’ayi ne Yahudawa suke da shi game da wuta da ke ci a kan bagade, amma mene ne Nassosi suka nuna? (it-1-E 833 ¶1)
L.Fi 6:25—Ta yaya hadayar wanke zunubi ta yi dabam da hadaya ta ƙonawa da hadaya ta gyaran zumunci? (si-E 27 ¶15)
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu game da Jehobah da wa’azi da dai sauransu?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) L.Fi 6:1-18 (th darasi na 5)
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Haɗuwa ta Fari: (minti 3 ko ƙasa da hakan) Ka soma da bin bayanin da ke Yadda Za Mu Yi Wa’azi. Sai ka nuna wa maigidan wani abu a Hasumiyar Tsaro ta 2 2020, sa’an nan ka ba shi mujallar. (th darasi na 3)
Komawa Ziyara: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Ka soma da bin bayanin da ke Yadda Za Mu Yi Wa’azi. Sai ka nuna wa maigidan dandalinmu, sa’an nan ka ba shi katin jw.org. (th darasi na 11)
Nazarin Littafi Mai Tsarki: (minti 5 ko ƙasa da hakan) bhs 178-179 sakin layi na 12-13 (th darasi na 6)
RAYUWAR KIRISTA
Ka Zama Abokin Jehobah—Ku Zama Masu Godiya: (minti 5) Ku kalli bidiyon. Sai ka gayyaci yara zuwa dakalin magana in zai yiwu, kuma ka yi musu tambayoyi game da bidiyon.
Bukatun Ikilisiya: (minti 10)
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30 ko ƙasa da hakan) ia babi na 22 sakin layi na 1-13
Kammalawa (minti 3 ko ƙasa da hakan)
Waƙa ta 37 da Addu’a