22-28 ga Nuwamba
ALƘALAI 1-3
Waƙa ta 126 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 1)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Labari Mai Daɗi da Ke Sa Ƙarfin Zuciya”: (minti 10)
Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah: (minti 10)
Alƙ 2:10-12—Me ya sa waɗannan ayoyin gargaɗi ne a gare mu? (w05 3/1 27 sakin layi na 7)
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu game da Jehobah da wa’azi da dai sauransu?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4) Alƙ 3:12-31 (th darasi na 5)
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
“Yadda Za Ka Daɗa Jin Daɗin Wa’azi—Ka Amince da Taimakon Jehobah ta Wurin Yin Addu’a”: (minti 10) Tattaunawa. Ku kalli bidiyon nan Za Ku Ji Daɗin Almajirtarwa Idan Kun Amince da Taimakon Jehobah—Addu’a.
Nazarin Littafi Mai Tsarki: (minti 5) lffi darasi na 02, gabatarwa da kuma batu na 1-3 (th darasi na 11)
RAYUWAR KIRISTA
Ka Zama Abokin Jehobah—Yadda Za Ka Yi Wa’azi da Kyau: (minti 5) Tattaunawa. Ku kalli bidiyon. Idan zai yiwu, ka zaɓi yara zuwa kan bagadi kuma su amsa tambayoyin nan: Ta yaya za mu yi shiri don wa’azi? Ta yaya za mu yi adon da ya dace? Ta yaya za mu nuna halin kirki sa’ad da muke wa’azi?
“Yadda Za A Yi Taron Fita Wa’azi da Kyau”: (minti 10) Tattaunawa da mai kula da hidima zai yi. Ka ba ’yan’uwa dama su faɗi abin da ya sa yake da muhimmanci su isa taron fita wa’azi da wuri.
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) lfb darasi na 59
Kammalawa (minti 3)
Waƙa ta 29 da Addu’a