Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

KA YI WA’AZI DA KWAZO | YADDA ZA KA DAƊA JIN DAƊIN WA’AZI

Ka Koya wa Dalibanka Yadda Za Su Rika Nazari da Kansu

Ka Koya wa Dalibanka Yadda Za Su Rika Nazari da Kansu

Don ka taimaka wa ɗalibanka su san Jehobah kuma su manyanta, wajibi ne su ƙara koyan wasu abubuwa. (Mt 5:3; Ibr 5:12–6:2) Wajibi ne su koyi yadda za su riƙa nazari da kansu.

Tun da farko ka nuna wa ɗalibanka yadda za su riƙa shiri kafin ku yi nazari, kuma ka ƙarfafa su su yi hakan. (mwb18.03 6) Ka ƙarfafa su su yi addu’a kafin su soma nazari da kansu. Ka taimaka musu su san yadda ake amfani da waya a nazari. Ka bayyana musu yadda za su ga sabbin abubuwa a dandalin jw.org da kuma shirye-shiryen JW. Ka ci gaba da koya musu yadda za su riƙa karanta Littafi Mai Tsarki kullum, da yin shiri don taro da kuma yin bincike don su sami amsoshin tambayoyinsu. Ka taimaka musu su riƙa yin tunani a kan abin da suke koya.

KU KALLI BIDIYON NAN KU TAIMAKA WA ƊALIBANKU SU RIƘA NAZARI DA KANSU, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Ta yaya Anita ta taimaka wa Rose ta san cewa yin nazari ba kawai sanin amsar tambayoyi ba ne?

  • Mene ne ya taimaka wa Rose ta amince cewa ya dace da Jehobah ya hana yin lalata?

  • Ka koya wa ɗalibanka yadda za su riƙa nazari da kansu don abin da suke koya ya ratsa zuciyarsu

    Mene ne Rose ta fahimta game da muhimmancin yin tunani a kan abin da take nazarinsa?