DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
Jehobah Mai Haƙuri Ne, Amma Yana Hukunta Waɗanda Suka Ƙi Tuba
Jehobah ya ƙyale Assuriyawa su ci Israꞌilawa a yaƙi (2Sar 17:5, 6; w05 12/1 15 sakin layi na 16)
Jehobah ya hukunta mutanensa domin sun ci gaba da yi masa rashin biyayya (2Sar 17:9-12; w12 4/1 10 sakin layi na 2; w01 11/1 22 sakin layi na 10)
Jehobah ya yi haƙuri da Israꞌilawan kuma ya yi ta yi musu gargaɗi (2Sar 17:13, 14)
Ubanmu na sama yana haƙuri da ꞌyan Adam da yake mu ajizai ne. (2Bi 3:9) Amma don ya cim ma nufinsa, zai ɗauki mataki don ya halaka mugaye nan ba da daɗewa ba. Ta yaya hakan zai motsa mu mu yi waꞌazi da gaggawa kuma mu yi biyayya saꞌad da aka yi mana gyara?