RAYUWAR KIRISTA
Ku Kasance da Tabbaci Cewa Za Mu Tsira a Ƙarshen Zamanin Nan
Nan ba da daɗewa ba, Jehobah zai daina haƙuri da masu mugunta na wannan zamanin. Za a halaka addinan ƙarya kuma alꞌumman da suka haɗa kai za su kai wa mutanen Allah hari, saꞌan nan Jehobah zai halaka mugaye a yaƙin Armageddon. Kiristoci suna marmarin ganin lokacin da waɗannan abubuwa masu muhimmanci za su faru.
Hakika, ba mu san yadda abubuwa za su faru dalla-dalla a lokacin ƙunci mai girma ba. Alal misali, ba mu san ainihin lokacin da za a soma ƙunci mai girma ba. Ba mu san dalilan da gwamnatoci za su ba da don su kai wa addinai hari ba. Ba mu san tsawon lokacin da harin da alꞌummai za su kai wa mutanen Allah zai ɗauka ba ko kuma abin da hakan ya ƙunsa ba. Ban da haka ma, ba mu san ainihin yadda Jehobah zai halaka mugaye a Armageddon ba.
Amma, Littafi Mai Tsarki ya ba mu dukan bayanan da muke bukata don mu kasance da tabbaci da kuma ƙarfin zuciya game da abubuwan da za su faru a nan gaba. Alal misali, mun san cewa muna rayuwa a ƙarshen “kwanakin ƙarshe.” (2Ti 3:1) Kuma mun san “za a rage kwanakin” da za a kai wa addinai hari don kada a halaka addini na gaskiya. (Mt 24:22) Muna da tabbaci cewa Jehobah zai ceci mutanensa. (2Bi 2:9) Ƙari ga haka, mun san cewa Wanda Jehobah ya zaɓa don ya halaka mugaye kuma ya kāre taro mai girma a yaƙin Armageddon mai adalci ne kuma yana da iko sosai.—R. Yar 19:11, 15, 16.
Abubuwan da za su faru a nan gaba za su sa mutane su “suma don tsoro.” Amma idan muna karanta da kuma yin bimbini game da yadda Jehobah ya ceci mutanensa a dā, da abubuwan da ya bayyana za su faru a nan gaba, hakan zai sa mu ‘shirya kanmu sosai’ domin cetonmu ya yi kusa.—Lu 21:26, 28.