RAYUWAR KIRISTA
Ku Yi Farin Ciki Idan Ana Tsananta Muku
Za a tsananta wa Kiristoci. (Yoh 15:20) Ko da yake tsanantawa yana iya sa mu baƙin ciki da alhini a wasu lokuta, za mu yi farin ciki idan muka jimre.—Mt 5:10-12; 1Bi 2:19, 20.
KU KALLI BIDIYON NAN ZAI YIWU MU YI FARIN CIKI KO DA ANA TSANANTA MANA, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:
Mene ne muka koya daga labarin Ɗanꞌuwa Bazhenov game da muhimmancin
-
karatun Littafi Mai Tsarki kullum?
-
samun taimako daga wurin ꞌyanꞌuwanmu Kiristoci? a
-
adduꞌa a kowane lokaci?
-
rera waƙoƙinmu?
-
tattaunawa game da bangaskiyarmu?
a Za mu iya yin adduꞌa a madadin ꞌyanꞌuwanmu Kiristoci da suke kurkuku, za mu ma iya ambata sunayensu. Amma ba zai yiwu rashen ofishinmu ya tura musu wasiƙunmu ba.