RAYUWAR KIRISTA
Abin da Zai Taimaka Maka Ka Guji Yin Jinkiri
Mai yawan jinkiri ba ya yin abin da ya kamata ya yi nan da nan. Jehu bai yi jinkiri ba saꞌad da Jehobah ya gaya masa ya kashe dukan mutanen gidan Ahab. (2Sar 9:6, 7, 16) Wasu za su iya cewa: “Wataƙila zan yi baftisma nan da ꞌyan shekaru masu zuwa.” Ko “Zan soma karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana nan ba da daɗewa ba.” Ko kuma “Zan soma majagaba na kullum da zarar na sami aikin da ake biyan albashi mai tsoka.” Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka mana mu guji yin jinkiri a ayyukan ibadarmu.
Ta yaya waɗannan ayoyin za su sa mu guji yin jinkiri?
-
M. Wa 5:4
-
M. Wa 11:4
-
1Ko 7:29-31
-
Yak 4:13, 14