Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Adduꞌoꞌinmu Suna da Muhimmanci ga Jehobah

Adduꞌoꞌinmu Suna da Muhimmanci ga Jehobah

Adduꞌoꞌinmu suna kamar turare mai ƙamshi da ake ƙonawa a kai a kai ga Jehobah a haikali. (Za 141:2) Idan muka nuna wa Ubanmu na sama ƙaunarmu da godiyarmu ta wurin gaya masa damuwarmu da abubuwan da muke so, kuma muka nemi ja-gorancinsa, hakan zai nuna mun daraja dangantakarmu da shi. Hakika, Jehobah yana ɗaukan gajerun adduꞌoꞌin da ake yi a taronmu a matsayin bauta mai muhimmanci a gare shi. Amma, saꞌad da muke adduꞌa mu kaɗai, Jehobah yana farin ciki idan muka ɗauki dogon lokaci muka gaya masa yadda muke ji da dukan zuciyarmu!​—K. Ma 15:8.

KU KALLI BIDIYON NAN INA SON YIN ADDUꞌA SOSAI, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Waɗanne ayyuka ne Ɗanꞌuwa Johnson ya yi a ƙungiyar Jehobah?

  • Ta yaya adduꞌoꞌin Ɗanꞌuwa Johnson suka nuna ya dogara ga Jehobah?

  • Waɗanne darussa ne muka koya daga labarin Ɗanꞌuwa Johnson?