16-22 ga Disamba
ZABURA 119:57-120
Waƙa ta 129 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)
1. Yadda Za Mu Jimre da Matsaloli
(minti 10)
Ku ci-gaba da karanta da kuma yin nazarin Kalmar Allah (Za 119:61; w06 7/1 shafi na 8 sakin layi na 2; w00 12/1 shafi na 24 sakin layi na 3)
Wahala za ta iya koya mana mu dogara sosai ga Jehobah (Za 119:71; w06 9/1 shafi na 29 sakin layi na 4)
Ku dogara ga Jehobah don ya taimaka muku (Za 119:76; w17.07 shafi na 13 sakin layi na 3 da 5)
KA TAMBAYI KANKA, ‘A waɗanne hanyoyi ne Jehobah ya taimaka mini in jimre da matsalolina?’
2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah
(minti 10)
-
Za 119:96—Mene ne mai yiwuwa wannan ayar take nufi? (w06 9/1 shafi na 29 sakin layi na 5)
-
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu?
3. Karatun Littafi Mai Tsarki
(minti 4) Za 119:57-80 (th darasi na 12)
4. Fara Magana da Mutane
(minti 3) WAꞌAZI GIDA-GIDA. Ka nuna wa maigidan dandalinmu, kuma ka ba shi katin jw.org. (lmd darasi na 2 batu na 5)
5. Komawa Ziyara
(minti 4) SAꞌAD DA KAKE AYYUKA NA YAU DA KULLUM. Ka gayyaci mutumin zuwa jawabi ga jamaꞌa da za a yi a nan gaba. Ka nuna masa bidiyon nan Me Ake Yi a Majamiꞌar Mulki? (lmd darasi na 8 batu na 3)
6. Ka Bayyana Imaninka
(minti 5) Gwaji. Ijwbq talifi na 157—Jigo: Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Balaꞌi? (lmd darasi na 3 batu na 3)
Waƙa ta 128
7. Jehobah Yana Taimaka Mana Mu Iya Jimrewa
(minti 15) Tattaunawa.
Jimrewa tana nufin mu bi da yanayi mai wuya ba tare da mun yi sanyin gwiwa ba. Yana kuma nufin mu tsaya daram, mu kasance da raꞌayin da ya dace da begen cewa abubuwa za su gyaru a nan gaba. Idan mun kasance da halin jimiri, ba za mu “ja da baya” ko mu yi sanyi a ibadarmu saꞌad da muka fuskanci matsaloli ba. (Ibr 10:36-39) Jehobah yana a shirye ya taimaka mana mu jimre da matsaloli.—Ibr 13:6
Kusa da kowane nassi da ke gaba, ka rubuta yadda Jehobah ya taimaka maka ka jimre.
-
Lu 11:13
-
Ro 8:25
-
1Ta 5:11
-
Yak 1:5
Ku kalli BIDIYON Ku Yi Addu’a Don Wadanda Suke Shan Wahala. Sai ka tambayi masu sauraro:
-
Ta yaya za mu yi amfani da dandalin jw.org don mu san ꞌyanꞌuwanmu da suke fama da matsaloli?
-
Ta yaya iyaye za su koya wa yaransu adduꞌa, kuma me ya sa yin hakan yake da muhimmanci?
-
Me ya sa yana da muhimmanci mu roƙi Jehobah ya taimaka wa ꞌyanꞌuwanmu su iya jimrewa?
-
Ta yaya yin adduꞌa a madadin wasu yake taimaka mana mu iya jimre matsalolinmu?
8. Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya
(minti 30) kr babi na 21 sakin layi na 8-14