18-24 ga Nuwamba
ZABURA 107-108
Waƙa ta 7 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)
1. “Ku Yi Godiya ga Yahweh, Gama Shi Mai Alheri Ne”
(minti 10)
Kamar yadda Jehobah ya ceci Israꞌilawa daga hannun Babila, ya kuɓutar da mu daga duniyar Shaiɗan (Za 107:1, 2; Kol 1:13, 14)
Yin godiya ga Jehobah zai sa mu yabe shi a cikin ikilisiya (Za 107:31, 32; w07 5/1 shafi na 6 sakin layi na 2)
Za mu ci gaba da gode ma Jehobah idan muna tuna irin alherin da yake mana (Za 107:43; w15 1/15 shafi na 9 sakin layi na 4)
2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah
(minti 10)
-
Za 108:9—Yaushe ne mai yiwuwa wannan ayar ta cika? (it-2-E 420 sakin layi na 4)
-
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu?
3. Karatun Littafi Mai Tsarki
(minti 4) Za 107:1-28 (th darasi na 5)
4. Fara Magana da Mutane
(minti 3) SAꞌAD DA KAKE AYYUKA NA YAU DA KULLUM. (lmd darasi na 1 batu na 4)
5. Komawa Ziyara
(minti 4) SAꞌAD DA KAKE AYYUKA NA YAU DA KULLUM. Ka gaya wa mutumin yadda muke nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane, kuma ka ba shi katin nazarin Littafi Mai Tsarki. (lmd darasi na 9 batu na 3)
6. Jawabi
(minti 5) ijwyp talifi na 90—Jigo: Ta Yaya Zan Guji Mugun Tunani? (th darasi na 14)
Waƙa ta 46
7. Muna Rera Waƙa don Mu Yabi Jehobah
(minti 15) Tattaunawa.
Bayan da Jehobah ya ceci Israꞌilawa daga sojojin Masar a Jar Teku, bayinsa sun rera waƙar yabo. (Fit 15:1-19) Mazan ne suka soma rera sabuwar waƙar. (Fit 15:21) Yesu da ꞌyanꞌuwa a ƙarni na farko ma sun rera waƙar yabo ga Allah. (Mt 26:30; Kol 3:16) Muna ci gaba da nuna godiyarmu ga Jehobah ta wajen yin waƙar yabo a taron ikilisiya da kuma manyan taronmu. Alal misali, waƙar da muka rera yanzu mai jigo, “Muna Godiya, Ya Jehobah,” tun daga shekara ta 1966 muke rera ta.
A wasu alꞌadu, maza suna jin kunyar yin waƙa a jamaꞌa. Wasu sukan yi jinkirin yin waƙa domin suna ganin ba su da murya mai kyau. Amma zai dace mu tuna cewa yin waƙa hanya ɗaya ce da muke yi wa Jehobah ibada. Ƙungiyarmu tana aiki tuƙuru don ta shirya kuma ta zaɓi waƙoƙin da suka dace a kowane taronmu. Abin da muke bukata mu yi kawai shi ne, mu haɗa muryoyinmu mu rera waƙa don mu nuna ƙauna da kuma godiyarmu ga Jehobah.
Ku kalli BIDIYON Tarihinmu da Ci gaban da Muka Samu—Kyautar Waka, Kashi na 2. Sai ka tambayi masu sauraro:
-
Mene ne ya faru a shekara ta 1944?
-
Ta yaya ꞌyanꞌuwanmu da ke ƙasar Siberia suka nuna godiyarsu ta wajen rera waƙoƙin Mulkin?
-
Me ya sa rera waƙoƙi yake da muhimmanci ga Shaidun Jehobah?
8. Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya
(minti 30) kr babi na 20 sakin layi na 1-6, akwatin da ke shafi na 211 da 214-215