Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

23-29 ga Disamba

ZABURA 119:​121-176

23-29 ga Disamba

Waƙa ta 31 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

1. Yadda Za Mu Guji Baƙin Ciki

(minti 10)

Ku Ƙaunaci Dokokin Allah (Za 119:127; w18.06 17 sakin layi na 5-6)

Ku guji yin zunubi (Za 119:128; w93-E 4/15 17 sakin layi na 12)

Ka saurari Jehobah kuma ka guji yin kura-kuran da “marar tunani” sukan yi (Za 119:​130, 133; K. Ma 22:3)

KA TAMBAYI KANKA, ‘Waɗanne gyara ne nake bukata in yi da zai taimaka mini in ƙaunaci dokokin Jehobah kuma in guji yin zunubi?’

2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah

(minti 10)

  • Za 119:160—Kamar yadda ayar nan ta faɗa, wane abu ne ya kamata mu gaskata da shi? (w23.01 2 sakin layi na 2)

  • A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu?

3. Karatun Littafi Mai Tsarki

(minti 4) Za 119:​121-152 (th darasi na 2)

KA YI WAꞌAZI DA ƘWAZO

4. Fara Magana da Mutane

(minti 3) WAꞌAZI GIDA-GIDA. (lmd darasi na 1 batu na 5)

5. Komawa Ziyara

(minti 4) WAꞌAZI GIDA-GIDA. Ka nuna wa mutumin yadda zai sami bayani a kan batun da yake so a dandalin jw.org. (lmd darasi na 8 batu na 3)

6. Almajirtarwa

(minti 5) Ka tattauna da ɗalibinka da ba ya halartan taro a kai a kai. (lmd darasi na 12 batu na 4)

RAYUWAR KIRISTA

Waƙa ta 121

7. Kada Ka Bar Son Kuɗi Ya Sa Ka Baƙin Ciki

(minti 15) Tattaunawa.

Waɗanda suke neman kuɗi ido a rufe sukan “jawo wa kansu baƙin ciki iri iri.” (1Ti 6:​9, 10) Idan muka sa neman kuɗi farko a rayuwarmu, za mu iya jawo ma kanmu matsalolin nan da aka ambata a gaba.

  • Ba za mu iya kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah ba. —Mt 6:24

  • Ba za mu taɓa gamsuwa ba.—M. Wa 5:10

  • Zai mana wuya mu guji yin zunubi har da ƙarya da sata da kuma yaudara. (K. Ma 28:20) Idan muka yi kuskure, zuciyarmu za ta soma daminmu ko hakan ya ɓata mana suna, ko kuma dangantakarmu da Allah ta yi tsami

Karanta Ibraniyawa 13:​5, sai ku tattauna tambayar da ke gaba:

  • Wane raꞌayi game da kuɗi ne zai taimaka mana kada mu jawo ma kanmu baƙin ciki, kuma me ya sa?

Ko da ba mu sa neman kuɗi farko a rayuwarmu ba, za mu iya jawo ma kanmu baƙin ciki idan ba ma kashe kuɗi a hanyar da ta dace.

Ku kalli bidiyon ZANEN ALLO Za Ku Yi Amfani da Kudinku da Kyau. Sai ka tambayi masu sauraro:

  • Me ya sa zai dace mu lissafta abubuwan da za mu saya, kuma ta yaya za mu yi hakan?

  • Me ya sa yake da kyau mu riƙa ajiye wasu kuɗaɗe?

  • Me ya sa yake da muhimmanci mu guji cin bashi?

8. Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya

Kammalawa (minti 3) | Waƙa ta 101 da Adduꞌa