25 ga Nuwamba–1 ga Disamba
ZABURA 109-112
Waƙa ta 14 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)
1. Ku Goyi Bayan Sarkinmu Yesu!
(minti 10)
Bayan da Yesu ya je sama, ya zauna a hannun damar Jehobah (Za 110:1; w06 9/1 shafi na 28 sakin layi na 6)
A shekara ta 1914 ne Yesu ya soma yin nasara a kan magabtansa (Za 110:2; w00 4/1 shafi na 25 sakin layi na 3)
Za mu iya yin iya ƙoƙarinmu wajen goyon bayan sarautar Yesu (Za 110:3; lff darasi na 55 batu na 1)
KA TAMBAYI KANKA, ‘Waɗanne makasudai ne zan kafa don in nuna cewa ina goyon bayan Mulkin?’
2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah
(minti 10)
-
Za 111:10—Mece ce hikima, kuma ta yaya muka sani cewa ba yawan shekarun mutum ba ne yake nuna cewa shi mai hikima ne? (w17.12 shafi na 20 sakin layi na 12)
-
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu?
3. Karatun Littafi Mai Tsarki
(minti 4) Za 109:1-26 (th darasi na 2)
4. Fara Magana da Mutane
(minti 2) WAꞌAZI GIDA-GIDA. Ka yi amfani da wata warƙa wajen soma tattaunawa da mutane. (lmd darasi na 4 batu na 3)
5. Ka Bayyana Imaninka
(minti 5) Gwaji. ijwfq talifi na 23—Jigo: Me Ya Sa Ba Ku Yaƙi? (lmd darasi na 4 batu na 4)
6. Almajirtarwa
Waƙa ta 72
7. Ta Yaya Za Mu Goyi Bayan Mulkin?
(minti 15) Tattaunawa.
Mulkin da Jehobah ya kafa ya nuna cewa shi ne mai sarautar sama da ƙasa. (Da 2:44, 45) Saboda haka, idan muka yi iya ƙoƙarinmu muka goyi bayan Mulkin Allah, muna nuna cewa Mulkinsa ne ya fi kyau.
Ku kalli BIDIYON Ku Goyi Bayan “Sarkin Salama” da Dukan Zuciyarku.” Sai ka tambayi masu sauraro:
-
Ta yaya muke goyon bayan Mulkin Allah?
Ka rubuta nassin da ya jitu da kowanne batu na gaba da ya nuna yadda muke goyon bayan Mulkin Allah.
-
Sa Mulkin farko a rayuwarmu.
-
Bin kaꞌidodin Mulkin.
-
Yin waꞌazin Mulkin da ƙwazo.
-
Daraja gwamnatocin ꞌyan Adam, amma idan suka ce mu yi wani abin da Allah ba ya so, ba za mu yi biyayya ba.
8. Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya
(minti 30) kr babi na 20 sakin layi na 7-16, da akwatin da ke shafi na 215