30 ga Disamba, 2024–5 ga Janairu, 2025
ZABURA 120-126
Waƙa ta 144 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)
1. Sun Yi Shuki da Wahala Amma Sun Yi Farin Ciki Saꞌad da Suke Girbin
(minti 10)
Israꞌilawa sun yi farin ciki saꞌad da aka sake su daga Babila su maido da bauta ta gaskiya (Za 126:1-3)
Mai yiwuwa waɗanda suka dawo Yahuda sun yi kuka don irin jan aiki da za su yi (Za 126:5; w04 6/1 shafi na 24 sakin layi na 10)
Mutanen sun nace a yin aikin kuma sun sami albarka (Za 126:6; w21.11 shafi na 24 sakin layi na 17; w01 8/1 shafi na 16 sakin layi na 13-14; ka duba hoton shafin farko)
DON BIMBINI: Bayan mun shiga sabuwar duniya, waɗanne ƙalubale ne za mu fuskanta saꞌad da muke aikin gyare-gyare da kwaskwarima? Waɗanne albarku ne za mu samu?
2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah
(minti 10)
-
Za 124:2-5—Shin, za mu zata cewa Jehobah zai kāre mu kamar yadda ya kāre alꞌummar Israꞌila? (cl 73 sakin layi na 15)
-
A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu?
3. Karatun Littafi Mai Tsarki
(minti 4) Za 124:1–126:6 (th darasi na 5)
4. Fara Magana da Mutane
(minti 3) WAꞌAZI A INDA JAMAꞌA SUKE. (lmd darasi na 3 batu na 5)
5. Komawa Ziyara
(minti 4) WAꞌAZI GIDA-GIDA. A makon da ya shige da ka zo, mutumin ya yi shakkar koyarwar Littafi Mai Tsarki. (lmd darasi na 9 batu na 5)
6. Almajirtarwa
Waƙa ta 155
7. Mu Yi Marmarin Ganin Cikar Alkawuran Allah
(minti 15) Tattaunawa.
Jehobah ya cika alkawarin da ya yi wa mutanensa da aka kai bauta a Babila. Ya cece su kuma ya gafarta musu zunubansu. (Ish 33:24) Ba shakka, ya kāre su da dabbobinsu daga zakuna da wasu dabbobi da suke wurin saꞌad da mutanen suka tafi bauta. (Ish 65:25) Yanzu, za su ji daɗin zama a gidajensu kuma su ci ꞌyaꞌyan gonakin inabinsu. (Ish 65:21) Allah ya albarkaci aikin hannuwansu kuma sun yi shekaru da yawa suna rayuwa.—Ish 65:22, 23.
Ku kalli BIDIYON Bari Alkawuran Allah Dangane da Salama Su Sa Ku Murna—Taƙaitawa. Sai ka tambayi masu sauraro:
-
A wace hanya muke ganin cikar waɗannan annabce-annabce a yau?
-
Ta yaya za su cika a idanunmu a sabuwar duniya?
-
Waɗanne alkawura ne kake marmarin ganin cikawarsu?
8. Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya
(minti 30) kr babi na 22 sakin layi na 1-7