Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

4-10 ga Nuwamba

ZABURA 105

4-10 ga Nuwamba

Waƙa ta 3 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

1. “Yana Tuna da Yarjejeniyarsa Har Abada”

(minti 10)

Jehobah ya yi wa Ibrahim alkawari, kuma ya maimaita alkawarin ga Ishaku da Yakub (Fa 15:18; 26:3; 28:13; Za 105:​8-11)

Mutane sun ɗauka cewa wannan annabcin ba zai taɓa cika ba (Za 105:​12, 13; w23.04 shafi na 28 sakin layi na 11-12)

Jehobah bai manta da alkawarin da ya yi wa Ibrahim ba (Za 105:​42-44; it-2-E 1201 sakin layi na 2)


KA TAMBAYI KANKA, ‘Ta yaya sanin cewa zan iya dogara ga Jehobah yake taimaka mini?’

2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah

(minti 10)

  • Za 105:4—Me ya sa ya kamata mu ‘biɗi Jehovah da ƙarfinsa’? (w00 3/1 shafi na 26 sakin layi na 6)

  • A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu?

3. Karatun Littafi Mai Tsarki

(minti 4) Za 105:​24-45 (th darasi na 5)

KA YI WAꞌAZI DA ƘWAZO

4. Fara Magana da Mutane

(minti 1) WAꞌAZI GIDA-GIDA. Maigidan ya shaƙu da ayyuka. (lmd darasi na 2 batu na 5)

5. Fara Magana da Mutane

(minti 2) WAꞌAZI GIDA-GIDA. Idan mutumin ya soma gardama, sai ka daina tattaunawa da shi cikin basira ba tare da faɗa ba. (lmd darasi na 4 batu na 5)

6. Komawa Ziyara

(minti 4) WAꞌAZI GIDA-GIDA. Ka ba mutumin wata mujalla da ke ɗauke da wani batu da ya so a farkon zuwan ka. (lmd darasi na 8 batu na 3)

7. Komawa Ziyara

(minti 4) SAꞌAD DA KAKE AYYUKA NA YAU DA KULLUM. Ka gaya wa mutumin game da manhajar JW Library® kuma ka taimaka masa wajen sauƙar da ita a wayarsa. (lmd darasi na 9 batu na 5)

RAYUWAR KIRISTA

Waƙa ta 84

8. Sadaukarwar da Kuke Yi Na Nuna Ƙaunarku

(minti 15) Tattaunawa.

Muna nuna ƙaunarmu ga Jehobah da kuma Sarkinmu Yesu ta wajen yin amfani da lokacinmu da ƙarfinmu da kuma dukiyarmu don mu yi ayyukan da suka shafi Mulkin. Hakan na faranta wa Jehobah rai kuma yana amfanar ꞌyanꞌuwanmu. (Yoh 14:23) Jerin talifofi nan “Yadda Ake Amfani da Gudummawarka” da ke dandalin jw.org na nuna yadda ꞌyanꞌuwanmu a duk faɗin duniya suna amfana daga gudummawarmu.

Ku kalli BIDIYON Gudummawarku Suna da Amfani Sosai. Sai ka tambayi masu sauraro:

  • Ta yaya yadda muke amfani da gudummawarmu wajen kāre ꞌyancinmu na ibada yana amfanar ꞌyanꞌuwanmu?

  • Ta yaya yadda ake amfani da gudummawar da ake samu yake taimakawa wajen gina Majamiꞌun Mulki?—2Ko 8:14

  • Waɗanne amfani ne muka samu daga yin amfani da gudummawarmu wajen fassara Littafi Mai Tsarki a harsuna da yawa?

9. Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya

Kammalawa (minti 3) | Waƙa ta 97 da Adduꞌa