Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

24-30 ga Oktoba

MISALAI 17-21

24-30 ga Oktoba
  • Waƙa ta 76 da Addu’a

  • Gabatarwar Taro (minti 3 ko ƙasa da hakan)

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

  • Ku Yi Zaman Lafiya da Mutane”: (minti 10)

    • Mis 19:11—Ka kwantar da hankalinka idan an ɓata maka rai (w14-E 12/1 12-13)

    • Mis 18:13, 17; 21:13—Ka tabbatar da cewa ka san ainihin abin da ya faru (w11 8/15 30 sakin layi na 11-14)

    • Mis 17:9—Ka nuna ƙauna ta wajen gafarta wa mutane (w11 8/15 31 sakin layi na 17)

  • Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 8)

    • Mis 17:5—Me ya sa ya kamata mu riƙa mai da hankali sosai wajen zaɓan nishaɗi? (w10 11/15 6 sakin layi na 17; w10 11/15 31 sakin layi na 15)

    • Mis 20:25—Ta yaya ƙa’idar nan ta shafi fita zance da kuma aure? (w09 5/15 15-16 sakin layi na 12-13)

    • Mene ne karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon ya koya mini game da Jehobah?

    • Waɗanne darussa ne na koya a karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon da zan iya yin amfani da su a wa’azi?

  • Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Mis 18:14–19:10

KA YI WA’AZI DA ƘWAZO

  • Haɗuwa ta Fari: (minti 2 ko ƙasa da hakan) Ka ba da takardar gayyata zuwa taro. (Takardar Gayyata)

  • Koma Ziyara: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Takardar Gayyata—Ka kammala ta wajen ambata bidiyon nan Me Ake Yi a Majami’ar Mulki?

  • Nazarin Littafi Mai Tsarki: (minti 6 ko ƙasa da hakan) lv 57 sakin layi na 14-15—Ka taimaki ɗalibin ya ga amfanin saka tufafin da ya dace da kuma yin ado mai kyau zuwa taro.

RAYUWAR KIRISTA

  • Waƙa ta 77

  • Zaman Lafiya Na Kawo Albarka: (minti 15) Tattaunawa. Ka saka bidiyon nan Zaman Lafiya Na Kawo Albarka. (A JW Library, ka duba ƙarƙashin LITTATTAFAI > BIDIYOYI > TARO DA HIDIMARMU.) Bayan haka, ka yi tambayoyin nan: Waɗanne abubuwa ne bai kamata mu yi ba sa’ad da wani ya ɓata mana rai? Wace albarka ce za mu samu idan muka bi shawarar da ke Misalai 17:9 da Matta 5:23, 24?

  • Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) kr babi na 2 sakin layi na 35-40, akwati da taswirar da ke shafi na 25-29

  • Bita da Abin da Za A Tattauna Mako Mai Zuwa (minti 3)

  • Waƙa ta 144 da Addu’a