Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

3-9 ga Oktoba

MISALAI 1-6

3-9 ga Oktoba
  • Waƙa ta 37 da Addu’a

  • Gabatarwar Taro (minti 3 ko ƙasa da hakan)

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

  • Ka Dogara ga Jehobah da Dukan Zuciyarka”: (minti 10)

    • [Ka saka bidiyon Gabatarwar Littafin Misalai.]

    • Mis 3:1-4—Ka nuna ƙauna da aminci (w00-E 1/15 23-24)

    • Mis 3:5-8—Ka dogara ga Jehobah da zuciya ɗaya (w00-E 1/15 24)

  • Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 8)

    • Mis 1:7—Ta yaya ne tsoron Allah shi ne “mafarin ilimi”? (w06 11/1 26 sakin layi na 5; it-2-E 180)

    • Mis 6:1-5—Me ya kamata mu yi idan muka fuskanci jarrabar yin sana’a marar kyau? (w00-E 9/15 25-26)

    • Mene ne karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon ya koya mini game da Jehobah?

    • Waɗanne darussa ne na koya a karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon da zan iya yin amfani da su a wa’azi?

  • Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Mis 6:20-35

KA YI WA’AZI DA ƘWAZO

  • Ka Shirya Gabatarwa na Wannan Watan: (minti 15) Tattaunawa. Ka saka bidiyon gabatarwar mujallu, sai ka tattauna wasu abubuwa a ciki. Ka ƙarfafa masu shela su saka hannu wajen gayyatar mutane zuwa taronmu na ƙarshen mako.

RAYUWAR KIRISTA

  • Waƙa ta 107

  • Bukatun Ikilisiya: (minti 8) Za ku iya tattauna darussan da kuka koya daga Yearbook. (yb16 25-27)

  • Ku Yi Alheri ga Mutanen da Suka Halarci Taronmu (Mis 3:27): (minti 7) Tattaunawa. Ka saka bidiyon nan Me Ake Yi a Majami’ar Mulki? (A JW Library, ka duba ƙarƙashin LITTATTAFAI > BIDIYOYI > TARO DA HIDIMARMU.) Bayan haka, ka sa masu sauraro su faɗi abubuwan da za mu iya yi don mu riƙa nuna ƙauna sosai a Majami’ar Mulki kullum, ba a watan Oktoba kaɗai ba.

  • Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) kr babi na 2 sakin layi na 1-12

  • Bita da Abin da Za A Tattauna Mako Mai Zuwa (minti 3)

  • Waƙa ta 143 da Addu’a