Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | MISALAI 1-6

‘Ka Dogara ga Jehobah da Dukan Zuciyarka’

‘Ka Dogara ga Jehobah da Dukan Zuciyarka’

Ya dace mu dogara ga Jehobah da zuciya ɗaya. Me ya sa? Domin ma’anar sunansa ta ba mu tabbaci cewa zai iya cika duk wani alkawarin da ya yi. Wani abu da yake taimaka mana mu dogara ga Jehobah shi ne yin addu’a. Misalai sura 3 ta tabbatar mana da cewa Jehobah zai ‘daidaita hanyoyinmu’ idan muka dogara gare shi.

Wanda yake ganin kansa mai hikima . . .

3:5-7

  • yakan yanke shawara ba tare da neman taimakon Jehobah ba

  • yakan dogara ga ra’ayinsa ko kuma na mutanen duniya

Wanda yake dogara ga Jehobah . . .

  • yakan ƙulla abota da shi ta wurin yin nazarin Littafi Mai Tsarki da bimbini da kuma addu’a

  • yakan nemi taimakon Allah ta wurin bincika nassosin Littafi Mai Tsarki sa’ad da yake yanke shawara

WANNE CIKIN WAƊANNAN NE YA KWATANTA YADDA NAKE YANKE SHAWARA?

NA FARKO: Ina yanke shawara a kan abin da nake gani ya dace

NA FARKO: Ina neman taimakon Jehobah ta wajen yin addu’a da kuma nazarin Littafi Mai Tsarki

NA BIYU: Ina addu’a Jehobah ya albarkaci shawarar da na yanke

NA BIYU: Ina yanke shawarar da ta jitu da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki