Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Kauna Ce Alamar Kiristoci na Gaskiya​—Ku Yi Murna da Gaskiya

Kauna Ce Alamar Kiristoci na Gaskiya​—Ku Yi Murna da Gaskiya

ME YA SA YAKE DA MUHIMMANCI: Wajibi ne mu gaya wa mutane game da nufin Allah kamar yadda Yesu ya yi. (Yoh 18:37) Ban da haka, wajibi ne mu riƙa murna da gaskiya da faɗin gaskiya da kuma yin abubuwan da suke da kyau duk da cewa muna rayuwa a duniyar da ba a yin hakan.​—1Ko 13:6; Fib 4:8.

YADDA ZA MU YI HAKAN:

  • Kada ka saurari ko ka yaɗa gulma don ka ɓata sunan wani.​—1Ta 4:11

  • Kada ka yi murna sa’ad da wani ya shiga cikin matsala

  • Ka riƙa yin abubuwan da za su taimaka ko ƙarfafa mutane

KU KALLI BIDIYON NAN “KU ƘAUNACI JUNA”​—KU YI MURNA DA GASKIYA, BA DA RASHIN ADALCI BA, SAI KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:

  • Ta yaya Debbie ta yi murna da rashin adalci?

  • Mene ne Alice ta faɗa da ya taimaka wa Debbie ta canja tunaninta?

  • Waɗanne abubuwa masu kyau ne za mu iya tattaunawa da mutane?

Ka yi murna da gaskiya ba da rashin adalci ba