FITOWA 37-38
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH |Bagadai da Ke Mazauni da Amfaninsu a Bauta Ta Gaskiya
37:25, 29; 38:1
An gina bagadan daidai da yadda Jehobah ya faɗa kuma suna da muhimmanci.
-
Jehobah yana jin daɗin addu’o’in da bayinsa suke masa kamar yadda yake jin daɗin turaren ƙonawa
-
Jehobah yana karɓan hadayun da aka yi a bagaden ƙona hadayu. Yadda aka yi bagaden a gaban mazaunin, ya nuna mana cewa dole ne mu ba da gaskiya ga hadayar Yesu don Jehobah ya amince da mu.—Yoh 3:16-18; Ibr 10:5-10
Ta yaya za mu sa addu’armu ta zama kamar turare mai ƙamshi a gaban Allah?—Za 141:2