RAYUWAR KIRISTA
Ka Daraja Dangantakarka da Jehobah
Shaidun Jehobah suna da wata gata na musamman. Da yake mu Kiristoci ne da muka yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma muka yi baftisma, muna da dangantaka mai kyau da Maɗaukaki Jehobah. Ya jawo mu wurinsa ta wurin Ɗansa. (Yoh 6:44) Kuma yana jin addu’o’inmu.—Za 34:15.
Ta yaya za mu kāre dangantakarmu da Allah? Zai dace mu guji abubuwa marasa kyau da Isra’ilawa suka yi. Jim kaɗan bayan da suka yi wa Jehobah alkawari cewa za su bauta masa shi kaɗai, sun yi ɗan maraƙi kuma suka bauta masa. (Fit 32:7, 8; 1Ko 10:7, 11, 14) Don haka, za mu iya tambayar kanmu: ‘Me zan yi idan na fuskanci jarraba? Abubuwan da nake yi suna nuna cewa ina daraja dangantakata da Jehobah?’ Ƙaunar da muke yi wa Ubanmu na sama za ta sa mu guji abubuwan da ya tsana.—Za 97:10.
KU KALLI BIDIYON NAN KA KĀRE DANGANTAKARKA DA JEHOBAH (KOL 3:5), SA’AN NAN KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:
-
Me kwaɗayi ya ƙunsa?
-
Me ya sa za mu guji kwaɗayi da bautar gumaka?
-
Wace alaƙa ke tsakanin zina da bautar gumaka?
-
Me ya sa ya zama dole waɗanda suke da ƙarin ayyuka a ƙungiyar Jehobah su mai da hankali wajen kula da bukatun matansu?