Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi—Karfafa Masu Son Sakonmu Su Halarci Taro

Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi—Karfafa Masu Son Sakonmu Su Halarci Taro

MUHIMMANCINSA: Taro yana ba mu zarafin ‘rera yabo’ ga Jehobah a kai a kai. (Za 149:1) Muna koyan yin nufin Allah a taronmu. (Za 143:10) Mutane suna yawan samun ci gaba da zarar sun soma halartar taronmu.

YADDA ZA MU CIM MA HAKAN:

  • Kada ka ɓata lokaci kafin ka gayyaci mutane zuwa taronmu. Ba ka bukatar ka jira har sai kun soma nazarin Littafi Mai Tsarki tare.—R. Yoh 22:17

  • Ka gaya wa mutumin yadda ake gudanar da taron da kuma abubuwan da za a tattauna a makon da zai halarta. Abubuwan nan za su iya taimaka: takardar gayyata zuwa taro, bidiyon nan Me Ake Yi a Majami’ar Mulki? da kuma darasi na 5 da 7 na ƙasidar nan Su Wane Ne Suke Yin Nufin Jehobah a Yau?

  • Ka taimaka. Shin mutumin zai bukaci taimako ne wajen zaɓan tufafin da suka dace don taron ko kuwa zai bukaci mu zo mu ɗauke shi da ababan hawanmu ko mu ba shi kuɗin mota? Ka zauna kusa da shi a taronmu kuma ku yi amfani da littattafanka idan bai da shi. Ka gabatar da shi ga wasu a cikin ikilisiyar