Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Ka Guji Abubuwan Nan Sa’ad da Kake Nazarin Littafi Mai Tsarki

Ka Guji Abubuwan Nan Sa’ad da Kake Nazarin Littafi Mai Tsarki

Yawan Magana: Ba dole sai ka bayyana kowane abu a babi ko sakin layin da kuke tattaunawa ba. Yesu ya yi amfani da tambayoyi wajen sa mutane su yi tunani don su fahimci wasu darussa. (Mt 17:24-27) Yin tambayoyi yana sa nazarin ya yi daɗi kuma yana taimaka wajen sa ka gane abin da ɗalibin ya yi imani da shi. (be 253 saki layi na 3-4) Zai dace ka yi haƙuri da ɗalibinka sa’ad da ka yi masa tambaya. Me ya kamata ka yi idan ɗalibin ya ba da amsar da ba ta dace ba? Ka yi masa wasu tambayoyi don ya fahimci batun da kansa. (be 238 sakin layi na 1-2) Kada ka cika magana da sauri domin ɗalibin ya sami zarafin koyan sabon abu.—be 230 sakin layi na 4.

Kada Ka Sa Nazarin Ya Yi Wuya: Bai kamata ka faɗi dukan abin da ka sani game da batun da kuke tattaunawa ba. (Yoh 16:12) Ka mai da hankali ga darussan da ke sakin layin. (be 226 sakin layi na 4-5) Yawan magana ko da mai daɗi ne zai iya sa ɗalibanmu su kasa fahimtar darussan. (be 235 sakin layi na 3) Da zarar ɗalibin ya fahimci darasin da ke sakin layin, ku ci gaba da sakin layi na gaba.

Kada Ku Nazarta Sakin Layi da Yawa: Maƙasudinmu ba yin nazarin sakin layi da yawa ba ne amma sa ɗalibin ya fahimci abin da muke nazarinsa ne. (Lu 24:32) Ka yi amfani da Kalmar Allah wajen mai da hankali ga wasu furucin Littafi Mai Tsarki da suka nuna darussan. (2Ko 10:4; Ibr 4:12; be 144 sakin layi na 1-3) Ka yi amfani da misalai masu sauƙi. (be 245 sakin layi na 2-4) Ka yi la’akari da abin da ɗalibin yake fama da shi da kuma imaninsa don ka san yadda za ka taimaka masa ya fahimci batun. Ka yi tambayoyi kamar su: “Mene ne ra’ayinka game da abin da ka koya a nan?” “Mene ne wannan batun ya koya mana game da Jehobah?” “Shin kana gani za ka amfana kuwa idan ka yi amfani da wannan shawarar?”—be 238 sakin layi na 3-5; 259 sakin layi na 1.