Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | ZABURA 135-141

Kirarmu Abin Al’ajabi Ne

Kirarmu Abin Al’ajabi Ne

Dauda ya yi bimbini a kan halaye masu kyau na Allah da ke a bayyane a halittunsa. Ya yi amfani da rayuwarsa wajen bauta wa Jehobah da gaba gaɗi.

Yin tunani sosai a kan halittu ya motsa Dauda ya yabi Jehobah:

139:14

  • “Zan yi godiya gareka; gama ƙirata abin ban tsoro ce, abin al’ajabi ce kuwa”

139:15

  • “Yanayina ba a ɓoye yake a gareka ba, sa’ad da aka yi ni a fakaice, sa’ad da aka sifanta ni da gwaninta daga cikin zurfafan duniya”

139:16

  • “Idanunka sun ga gaɓaɓuwan jikina tun ba su cika ba, a cikin littafinka an rubuta dukansu”