Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Idan Karamin Yaro Ne a Gida

Idan Karamin Yaro Ne a Gida

Idan muna wa’azi kuma muka tarar da ƙaramin yaro a gida, zai dace mu ce muna so mu yi magana da iyayensa. Hakan zai nuna cewa ba mu rena su ba. (Mis 6:20) Idan yaron ya ce mu shigo ciki, kada mu amince da hakan. Idan iyayensa ba sa gida, mu ce za mu sake dawowa.

Idan yaron ya yi girma, wataƙila yana tsakanin shekara sha biyar zuwa sha tara, zai dace mu nemi ganin iyayensa. Amma idan ba sa gida, muna iya tambaya ko iyayensa suna amincewa ya zaɓi littattafan da zai karanta. Idan ya ce e, za mu iya ba shi littattafai kuma mu nuna musu dandalin jw.org.

Idan mun koma ziyara wurin matashin da ya so saƙonmu, zai dace mu ce muna so mu ga iyayensa. Hakan zai ba mu zarafin gaya musu dalilin da ya sa muka zo kuma za mu nuna musu shawarwari masu kyau da ke cikin Littafi Mai Tsarki game da iyalai. (Za 119:86, 138) Nuna cewa mun daraja da kuma ladabta iyayen zai zama shaida mai kyau kuma zai iya ba mu wani zarafin tattaunawa da iyalin.—1Bi 2:12.