Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | ZABURA 119

Ka Yi “Tafiya Cikin Shari’ar Ubangiji”

Ka Yi “Tafiya Cikin Shari’ar Ubangiji”

Yin tafiya cikin shari’ar Jehobah yana nufin bin ƙa’idodinsa da zuciya ɗaya. Muna da misalai masu kyau a cikin Littafi Mai Tsarki na mutanen da suka bi dokar Jehobah kuma suka dogara gare shi kamar marubucin zaburar nan.

Za mu yi farin ciki na gaske idan muka bi dokar Allah

119:1-8

Joshua ya bi dokar Jehobah da zuciya ɗaya. Ya san cewa idan har yana son ya yi farin ciki da gaske, yana bukatar ya dogara ga Jehobah da dukan zuciyarsa

Kalmar Allah tana taimaka mana mu jimre da matsaloli

119:33-40

Irmiya ya kasance da gaba gaɗi kuma ya dogara ga Jehobah sa’ad da yake cikin mawuyacin hali. Ya yi rayuwa mai sauƙi kuma ya yi aikin da aka ba shi da ƙwazo

Sanin Kalmar Allah da kyau yana sa mu yi wa’azi da gaba gaɗi

119:41-48

Bulus bai ji tsoron yi wa mutane wa’azi ba. Ya dogara ga Jehobah sa’ad da yake yi wa Gwamna Filikus wa’azi da gaba gaɗi

A waɗanne yanayoyi ne zan iya dogara ga Jehobah sa’ad da nake wa’azi?

  • Makaranta

  • Aiki

  • Iyali

  • Wani wuri