10-16 ga Satumba
YOHANNA 3-4
Waƙa ta 57 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 3 ko ƙasa da hakan)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“Yesu Ya Yi Ma Wata Basamariya Wa’azi”: (minti 10)
Yoh 4:6, 7—Ko da yake Yesu ya gaji, ya nemi lokaci don ya yi ma wata Basamariya wa’azi (mwbr18.09-HA an ɗauko daga nwtsty a kan Yoh 4:6)
Yoh 4:21-24—Hirar da Yesu ya yi da wata mata ne ya sa mutane da yawa suka ji wa’azinsa
Yoh 4:39-41—Ƙwazon da Yesu ya yi ne ya sa Samariyawa da yawa suka ba da gaskiya a gare shi
Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 8)
Yoh 3:29—Mene ne ma’anar wannan ayar? (mwbr18.09-HA an ɗauko daga nwtsty)
Yoh 4:10—Ta yaya Basamariyar ta fahimci furucin nan “ruwa mai ba da rai” da Yesu ya yi, amma me Yesu yake nufi? (mwbr18.09-HA an ɗauko daga nwtsty)
Mene ne karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon ya koya maka game da Jehobah?
Waɗanne darussa ne kuma ka koya a karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Yoh 4:1-15
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Haɗuwa ta Fari: (minti 2 ko ƙasa da hakan) Ka bi bayanin da ke Yadda Za Mu Yi Wa’azi.
Bidiyon Komawa Ziyara ta Farko: (minti 5) Ka nuna bidiyon kuma ku tattauna shi.
Jawabi: (minti 6 ko ƙasa da hakan) wp16.2-E 9 sakin layi na 1-4—Jigo: Abin da Yohanna 4:23 Yake Nufi.
RAYUWAR KIRISTA
“Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi—Yin Hira da Mutane da Zai Kai ga Yin Wa’azi”: (minti 15) Tattaunawa. A ƙarshe, ka ƙarfafa ’yan’uwa su soma tattaunawa da mutane a makon, don su sami damar ba da labarin yadda suka yi hakan a taron Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu na gaba.
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) lv babi na 12 sakin layi na 15-22 da akwatin da ke shafi na 140
Bita da Abin da Za A Tattauna Mako Mai Zuwa (minti 3)
Waƙa ta 35 da Addu’a